
Tattaunawa kan darusan aka koya daga zaɓen gwamnan Osun
A Najeriya, Gwamnan mai ci kuma ɗan takarar jam’iyyar Accord Ademola Adeleke ya lashe zaɓen jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar da sama da kuri’u dubu 511, yayin da abokin karawarsa na APC mai mulkin ƙasar Bola Oyebamiji ya zo na biyu da banbancin kuri’u 66,252. Kafin ranar zaɓen dai an fuskanci dambarwar siyasa da rikece-rikece da suka yi sanadin mutuwar kusan mutum 40. Shiga alamar sauti don sauraron cikakkiyar da Ahmad Abba ya yi da Farfasa Kamilu Sani Fage, masanin siyasa kan zaɓen..
The skinny
The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.