
Dalilin da ya sanya aka fara haramta sana'ar jari bola a wasu sassan Najeriya
Sana’ar tattara wa da sayar da tsofaffin ƙarafa da sauran tarkace wadda aka fi sani da ‘Bola Jari’ na daga cikin sana’o’i da dubban mutane masamman matasa ke dogaro da su a Najeriya. Amma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sana’ar ta fuskanci babban ƙalubale, musamman saboda zargin cewa wasu masu tattara ƙarafa na amfani da ita wajen sayar da kayayyakin da aka sace daga tituna, gadoji, layin dogo da sauran muhimman abubuwan more rayuwa. Wannan ne ya sa wasu gwamnatocin jihohi suka ɗauki matakin dakatarwa ko haramta sana’ar baki ɗaya. Yanzu haka Ƙungiyar masu sana’ar ta jari bola ta yi…
The skinny
The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.