skinny.

Latest / Bakonmu a Yau

Tattaunawa kan matsalar hare-haren ƴanbindiga a makarantun Najeriya

Matsalar tsaro ta hare-haren da ‘yan ta’adda kan kai wa makarantu ko ɗalibai a sassan Najeriya, na ci gaba da ci wa al’ummar ƙasar tuwo a ƙwarya, la’akari da cewar ko a baya bayan nan, ‘yan bindiga sun kai hari tare da sace wasu ɗaliban wata Sakandare a ƙaramar hukumar Dekina da ke jihar Kogi. Wannan ya zo ne bayan hare-haren da a makwannin baya makarantun suka fuskanta a jihohin Oyo da kuma Borno. Kan haka Nura Ado Suleiman ya tattauna da shugaban ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya, Comrade Audu Titus Amba. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

The skinny

The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.