skinny.

Latest / Bakonmu a Yau

Dalilan da suka sa adadin amfanin gonar da Najeriya ke fitarwa ketare ya ragu

Wasu sabbin alƙaluma da ƙwararru suka fitar, sun nuna cewa adadin amfanin gonar da ake fitarwa daga Najeriya zuwa ƙasashen ƙetare ya ragu da aƙalla kaso 31 cikin 100, sakamakon yadda ƙasashe musamman na Turai da Asiya ke ƙin karɓar kayayyakin abincin, ciki har da Wake da Zoɓo da dai sauransu. Rahoton dai ya bayyana amfani da magungunan kashe ƙwari fiye da kima, a matsayin ɗaya daga cikin dalilan da ke kan gaba wajen janyowa Najeriya wannan hasara. Shiga alamar sauti don sauraron hirar da Nura Ado Suleimane ya yi da Farfesa Shehu Ado Garki, tsohon shugaban Jami’ar Al-Qalam da ke jihar Katsina…

The skinny

The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.