
Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata cibiyar da ke sa’ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka. Cibiyar ta ce adaɗin ya zarce jimillar kuɗin da aka ware wa manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya guda bakwai. Batu da ya janyo ce-ce-ku-ce. A cikin rahotonta, Cibiyar ta nuna cewa gwamnatin ta ware kusan…
The skinny
The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.