
Muna iyaka ƙoƙarinmu wajen ganin an yi zaɓen Osun ba tare da matsala ba - INEC
A ranar Asabar 15 ga watan Agustan 2026 ake sa ran gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun, wanda tuni ya yi sanadin halaka mutane sama da 30 a lokacin yaƙin neman zaɓe. Rundunar 'Yansanda dai ta tura muƙaddashin Sifeto Janar Isyaku Muhammmad da Kwamishinoni 30 da kuma wasu ƙarin jami'ai dubu 15,000, domin tabbatar da tsaron masu kaɗa ƙuri'u da jami'an zaɓen. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Zainab Aminu Abubakar, mai magana da yawun hukumar zaɓen ta Najeriya.
The skinny
The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.