skinny.

Latest / Bakonmu a Yau

Rakiya Sa'idu akan cika wa'adin korar baƙi a Afirka ta Kudu

An shiga wani yanayi na fargaba da tsananin tashin hankali a Afirka ta Kudu, yayin da yau wa’adin ranar 30 ga watan nan na Yuni ke cika, game da zanga-zangar da wasu ƙungiyoyin ƙyamar baki suka shirya don tilasta wa baƙin da ba su da takardu barin ƙasar. Ko da yake hukumar ’yansandan ƙasar ta ce ta tura ɗimbin jami'an tsaro zuwa yankunan da ake sa ran za su fuskanci tashin hankali, kamar su Pretoria, Johannesburg, da KwaZulu-Natal. Shamsiyya Haruna ta tattauna da Hajiya Rakiya Sa’idu, wata yar Najeriya da ke aiki a jami’ar Cape Town a Afirka ta Kudun, dangane da halin da suke ciki.

The skinny

The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.