
Dalilan da suka sa ƙasashe ke rububin ƙulla alaƙa da Ɗangote
Fitaccen attajirin Najeriya Aliko Ɗangote yau ya zama fuskar Afrika a harkokin kasuwanci, da zuba hannayen jari, inda shugabannin ƙasashen Duniya ke nemansa ruwa a jallo domin zuba jari a ƙasashensu ta hanyar samar da masana'antu. Bayan samar da gagarumar matatar man fetur a Najeriya, a kan dala biliyan 20, wadda a yau kimarta ya zarce Dala biliyan 40, yanzu haka ya fara aikin faɗaɗa ta domin zama mafi girma a Duniya, baya ga shirinsa na gina wata sabuwar matatar man a Gabashin Afrika. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziƙi, Hon Sama'ila Muhammad, a kan wannan shahara ta…
The skinny
The skinny isn't ready yet — notes appear once the transcript is processed.